Ezekiyel 38:1-7
1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, ka fuskanci Gog, na ƙasar Magog, babban sarkin Meshek da Tubal; ka yi annabci a kansa
3
ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.
4
Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in fitar da kai tare da dukan sojojinka, dawakanka, mahayan dawakanka saye da makamai, da kuma jama’a mai girma masu riƙe da garkuwoyi manya da ƙanana, dukansu da takuba a zāre.
5
Farisa, Kush da Fut za su kasance tare da su, duka riƙe da garkuwoyi da hulunan kwano,
6
haka ma Gomer da dukan sojojinsa, da Bet Togarma daga can arewa tare da dukan sojojinsa, al’ummai masu yawa tare da kai.
7
“ ‘Ka shirya; ka kintsa, kai da dukan jama’arka da suka taru kewaye da kai, ka kuma zama mai ba su umarni.
Settings