Ezekiyel 21:6-12
6
“Saboda ka yi nishi, ɗan mutum! Yi nishi a gabansu da ajiyar zuciya da ɓacin rai.
7
Kuma sa’ad da suka tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Domin labarun da suke fitowa. Kowace zuciya za tă narke kowane hannu kuma ya gurgunta; kowane ruhu zai sume kowane gwiwa kuma ta rasa ƙarfi kamar ruwa.’ Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
8
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
9
“Ɗan mutum, yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “ ‘Takobi, takobi, wasasshe da kuma gogagge,
10
wasasshe don kisa, gogagge har yana walwal kamar walƙiya! “ ‘Kada ku yi farin ciki, hukunci yana zuwa, domin kowa ya ƙi jin abin da na yi gargaɗi a kai.
11
“ ‘An ba da wannan takobi don a goge, don a kama da hannu; an washe shi aka kuma goge, shiryayye don a yi kisa da shi.
12
Ka yi kuka ka yi makoki, ɗan mutum, gama yana gāba da dukan sarakunan Isra’ila. An jefa su ga takobi tare da jama’ata. Saboda haka ku buga ƙirjinku.
Settings