Skip to content
Ezekiyel 21:8-17

Ezekiyel 21:8-17

8
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
9
“Ɗan mutum, yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “ ‘Takobi, takobi, wasasshe da kuma gogagge,
10
wasasshe don kisa, gogagge har yana walwal kamar walƙiya! “ ‘Kada ku yi farin ciki, hukunci yana zuwa, domin kowa ya ƙi jin abin da na yi gargaɗi a kai.
11
“ ‘An ba da wannan takobi don a goge, don a kama da hannu; an washe shi aka kuma goge, shiryayye don a yi kisa da shi.
12
Ka yi kuka ka yi makoki, ɗan mutum, gama yana gāba da dukan sarakunan Isra’ila. An jefa su ga takobi tare da jama’ata. Saboda haka ku buga ƙirjinku.
13
“ ‘Gwaji tabbatacce zai zo. Kuma a ce sandan Yahuda, wanda takobi ya ƙi, ya ci gaba? In ji Ubangiji Mai Iko Duka.’
14
“Saboda haka fa, ɗan mutum ka yi annabci ka kuma tafa hannuwanka. Bari takobi ya yi sara sau biyu, har sau uku ma. Takobin kisa ne, takobi ne don kisa mai girma, zai kewaye su a kowane gefe.
15
Domin zukata su narke da yawa kuma su fāɗi, na tsai da takobin kisa a dukan ƙofofinsu. Kash! A sa ya haska kamar walƙiya, ana riƙe da shi don kisa.
16
Ya takobi, yi sara zuwa dama ka yi kuma zuwa hagu, duk inda aka juya ka.
17
Zan tafa hannuwana, fushina kuwa zai sauka. Ni Ubangiji na faɗa.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options