Fitowa 39:8-21
8
Suka yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, aikin gwani. Suka yi shi kamar efod, na zinariya, da na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da kuma na lallausan lilin.
9
Ƙyallen maƙalawa a ƙirjin murabba’i ne, aka ninka shi biyu, tsawonsa da fāɗinsa kamu ɗaya-ɗaya ne.
10
Sa’an nan suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na farko akwai yakutu, da tofaz, da zumurrudu;
11
a jeri na biyu akwai turkuwoyis, da saffaya, da daimon;
12
a jeri na uku akwai yakinta, da idon mage, da ametis;
13
a jeri na huɗu akwai beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.
14
Aka zāna duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowane sunan ’ya’yan Isra’ila goma sha biyu, kamar yadda akan yi hatimi.
15
Sai suka yi tuƙaƙƙun sarƙoƙi na zinariya zalla a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
16
Suka yi tsaiko biyu na zinariya da zoban zinariya biyu, suka kuma ɗaura zoban a kusurwoyi biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
17
Suka ɗaura sarƙoƙi biyu na zinariya da kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
18
Suka maƙala waɗancan bakin sarƙoƙin zinariya a tsaikon nan biyu, sa’an nan suka rataya su a kafaɗun efod daga gaba.
19
Suka yi zobai biyu na zinariya suka haɗa, suka sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji daga ciki kusa da efod.
20
Sa’an nan suka yi waɗansu ƙarin zobai biyu na zinariya, suka maƙale su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na efod kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar efod.
21
Suka ɗaura zoban ƙyallen maƙalawa a ƙirjin a zoban efod da shuɗiyar igiya don ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kwanta lif a bisa kan abin ɗamarar efod don kada yă kunce daga efod, sun yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Settings