Skip to content
Fitowa 38:1-7

Fitowa 38:1-7

1
Suka gina bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba’i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku.
2
Suka yi ƙahoni a kusurwansa huɗu, ƙahonin da bagade a haɗe suke, suka kuma dalaye bagaden da tagulla.
3
Da tagulla kuma ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta.
4
Suka yi wa bagaden raga, tagulla kuma don yă sa shi a tsakiya.
5
Suka yi zubin zoban tagulla don riƙe sanduna a kusurwoyi huɗu na ragar tagullar.
6
Suka yi sanduna da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da tagulla.
7
Suka sa sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefen bagade don ɗaukarsa, suka yi rami cikinsa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options