Fitowa 10:1-6
1
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu,
2
don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”
3
Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi ƙasƙantar da kanka a gabana? Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada.
4
In ka ƙi ka bari su tafi, gobe zan aiko da fāra a ƙasarka.
5
Za su rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za su cinye ɗan sauran abin da ya rage muku daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a gonakinku.
6
Za su cika gidajenka, da na fadawanka, da na dukan Masarawa, abin da iyayenka da kakanninka ba su taɓa gani ba, tun daga ranar da suka sami kansu a duniya, har yă zuwa yau.’ ” Sa’an nan Musa ya juya, ya rabu da Fir’auna.
Settings