Skip to content
Maimaitawar Shari’a 34:1-7

Maimaitawar Shari’a 34:1-7

1
Sai Musa ya hau Dutsen Nebo daga filayen Mowab, zuwa ƙwanƙolin Fisga, wanda yake ƙetare Yeriko. A can Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, daga Gileyad zuwa Dan,
2
da ta dukan Naftali, da yankin Efraim da na Manasse, dukan ƙasar Yahuda har zuwa Bahar Rum,
3
da Negeb da dukan yankin Kwarin Yeriko, Birnin Dabino, har zuwa Zowar.
4
Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, “Wannan ce ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, sa’ad da na ce, ‘Zan ba da ita ga zuriyarku.’ Na bar ka ka gani da idanunka, amma ba za ka haye zuwa cikinta ba.”
5
Nan fa, a ƙasar Mowab Musa bawan Ubangiji ya mutu, yadda Ubangiji ya faɗa.
6
Aka binne shi a Mowab, a kwarin kusa da Bet-Feyor, amma har wa yau babu wanda ya san inda kabarinsa yake.
7
Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa’ad da ya mutu, duk da haka idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuwa bai ragu ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options