Maimaitawar Shari’a 33:20-29
20
Game da Gad ya ce, “Mai albarka ne wanda ya fadada mazaunin Gad! Gad yana zama a can kamar zaki, yana yayyage a hannu da kai.
21
Ya zaɓi ƙasa mafi kyau wa kansa; aka ajiye masa rabon shugaba. Sa’ad da shugabannin mutane suka taru, ya aikata adalcin Ubangiji da kuma hukuncinsa game da Isra’ila.”
22
Game da Dan ya ce, “Dan ɗan zaki ne, yana tsalle daga Bashan.”
23
Game da Naftali ya ce, “Naftali ƙosasshe ne da tagomashin Ubangiji, ya kuma cika albarkarsa; zai gāji gefen kudu zuwa tafki.”
24
Game da Asher ya ce, “Mafi albarka na ’ya’yan, shi ne Asher; bari yă sami tagomashi daga ’yan’uwansa, bari kuma yă wanke ƙafafunsa a cikin mai.
25
Madogaran ƙofofinka za su zama ƙarfe da tagulla, ƙarfinka kuma zai zama daidai da kwanakinka.
26
“Babu wani kamar Allah na Yeshurun, wanda yake hawa a bisa sammai don yă taimake ka a kan gizagizai kuma a cikin darajarsa.
27
Allah madawwami shi ne mafakarka, a ƙarƙashina kuma madawwamin hannuwa ne. Zai kore abokin gābanka a gabanka, yana cewa, ‘Ka hallaka shi!’
28
Haka Isra’ila zai zauna lafiya shi kaɗai; zuriyar Yaƙub a tsare a ƙasar hatsi da sabon ruwan inabi, inda sammai za su zuba raɓa.
29
Kai mai albarka ne, ya Isra’ila! Wane ne yake kamar ka, mutanen da Ubangiji ya ceta? Shi ne mafakarka da mai taimakonka da kuma takobinka mai ɗaukaka. Abokan gābanka za su zo neman jinƙai a gabanka, za ka kuwa tattake masujadansu.”
Settings