Maimaitawar Shari’a 31:14
Ana nuna aya 14 tare da mahallin da ke kewaye.
11
sa’ad da dukan Isra’ila suka zo, don su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa, za ku karanta wannan doka a gabansu, a kunnuwansu.
12
Ku tattara mutane, maza, mata da kuma yara, da baƙin da suke zama a cikin garuruwanku, saboda su saurara, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su lura, su bi dukan kalmomin wannan doka.
13
’Ya’yansu, waɗanda ba su san wannan doka ba, dole su ji ta, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku muddin ranku a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.”
14
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu ranar mutuwarka ta yi kusa. Ka kira Yoshuwa, ku shigo Tentin Sujada, inda zan ba shi ragamar aiki.” Saboda haka Musa da Yoshuwa suka zo, suka kuma shiga Tentin Sujada.
15
Ubangiji kuwa ya bayyana a Tentin Sujada a cikin ginshiƙin girgije, sai girgijen ya tsaya a ƙofar Tentin Sujada.
16
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Za ka huta tare da kakanninka, waɗannan mutane kuwa ba da daɗewa ba za su yi karuwanci ga baƙin alloli na ƙasar da za su shiga. Za su yashe ni su kuma karya alkawarin da na yi da su.
17
A wannan rana zan yi fushi da su, in kuma yashe su; zan ɓoye fuskata daga gare su, za a kuwa hallaka su. Masifu masu yawa da wahaloli masu yawa za su auka musu, a wannan rana kuwa za su ce, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu’
Settings