Daniyel 11:2-9
2
“Yanzu dai, zan faɗa maka gaskiya. Sarakuna uku za su taso a Farisa, sa’an nan kuma na huɗu, wanda zai fi dukansu dukiya. Sa’ad da zai sami iko saboda dukiyarsa, zai zuga dukan kowane mutum yă yi gāba da masarautar Girka.
3
Sa’an nan wani babban sarki zai bayyana, wanda zai yi mulki da babban iko yă kuma yi abin da ya ga dama.
4
Bayan da ya bayyana, daularsa za tă wargaje za a rarraba ta zuwa kusurwoyi huɗu na duniya, a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, ba kuwa za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki daularsa a kuma ba wa waɗansu.
5
“Sai sarki Kudu zai yi ƙarfi ƙwarai, amma ɗaya daga cikin komandodinsa zai yi ƙarfi fiye da shi, zai kuma yi mulki masarautarsa da iko mai girma.
6
Bayan ’yan shekaru, za su haɗa kai. Diyar sarkin Kudu za tă je wurin sarkin Arewa ta sada zumunci, amma ba za tă riƙe iko ba, shi kuwa da ikonsa ba za su daɗe ba. A waɗannan kwanaki za a bashe ta, da ita da masu rakiyarta da kuma mahaifinta da kuma wanda ya goyi bayanta.
7
“Wani daga cikin zuriyarta zai taso yă ɗauki matsayinta. Zai kai wa sojojin sarkin Arewa hari yă kuma shiga kagararsa; zai yi yaƙi da su yă kuma yi nasara.
8
Zai ƙwace allolinsu, siffofinsu na ƙarfe da kuma kaya masu daraja na azurfa da na zinariya a kuma kai su Masar. Zai yi ’yan shekaru bai kai wa sarkin Arewa yaƙi ba.
9
Sa’an nan sarkin Arewa zai kai wa sarkin Kudu hari, amma zai janye, yă koma ƙasarsa.
Settings