Kolossiyawa 3:18-25
18
Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.
19
Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.
20
’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.
21
Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.
22
Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji.
23
Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba.
24
Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.
25
Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.
Settings