Ayyukan Manzanni 7:20-29
20
“A lokacin nan aka haifi Musa, shi kuwa ba kamar sauran jarirai ba ne. Wata uku aka yi renonsa a gidan mahaifinsa.
21
Sa’ad da aka ajiye shi a waje, diyar Fir’auna ta ɗauke shi ta kuma rene shi kamar ɗanta.
22
Musa ya sami ilimi cikin dukan hikimar Masarawa ya kuma zama mai iko cikin magana da ayyuka.
23
“Da Musa ya cika shekara arba’in da haihuwa, sai ya yanke shawara yă ziyarci ’yan’uwansa Isra’ilawa.
24
Ya ga ɗayansu yana shan wulaƙanci a hannun wani mutumin Masar, sai ya je ya kāre shi, ya rama masa ta wurin kashe mutumin Masar ɗin.
25
Musa ya yi tsammani mutanensa za su gane cewa, Allah yana amfani da shi don yă cece su, amma ba su gane ba.
26
Kashegari, Musa ya sadu da Isra’ilawa biyu suna faɗa. Ya yi ƙoƙari ya sasanta su, yana cewa, ‘Ku mutane, ku ’yan’uwa ne, don me kuke so ku cutar da juna?’
27
“Amma mutumin da yake wulaƙanta ɗayan, ya tura Musa a gefe ya ce, ‘Wa ya mai da kai mai mulki, da alƙali a kanmu?
28
Kana so ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan na jiya?’
29
Sa’ad da Musa ya ji haka, sai ya gudu zuwa ƙasar Midiyan, inda ya yi baƙunci, ya kuma haifi ’ya’ya biyu maza.
Settings