Ayyukan Manzanni 7:30-36
30
“Bayan shekaru arba’in suka wuce, sai mala’ika ya bayyana ga Musa cikin harshen wuta a ɗan itace a hamada kusa da Dutsen Sinai.
31
Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,
32
‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.
33
“Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, ‘Ka cire takalmanka; wurin da kake tsayen nan mai tsarki ne.
34
Tabbatacce na ga wulaƙancin da ake yi wa mutanena a Masar. Na ji nishinsu na kuma sauka domin in ’yantar da su. Yanzu ka zo, zan aike ka ka koma Masar.’
35
“Wannan Musa ɗin da suka ƙi suna cewa, ‘Wa ya mai da kai mai mulki da kuma alƙali?’ Allah da kansa ya aike shi, ta wurin mala’ikan da ya bayyana a gare shi a ɗan itace, yă zama mai mulkinsu, da kuma mai cetonsu.
36
Ya fitar da su daga Masar ya kuma yi ayyukan da abubuwan banmamaki a Masar, a Jan Teku, da kuma cikin hamada har shekara arba’in.
Settings