Skip to content
Ayyukan Manzanni 24:10-21

Ayyukan Manzanni 24:10-21

10
Da gwamna ya yi masa alama yă yi magana, sai Bulus ya amsa ya ce, “Na san cewa ka yi shekaru da yawa kana mulki a wannan ƙasa; saboda haka ina farin ciki in kāre kaina.
11
Da sauƙi za ka iya tabbatar cewa, bai fi kwana goma sha biyu da suka wuce ne na tafi Urushalima, domin yin sujada ba.
12
Masu zargina ba su same ni ina gardama da kowa a haikali, ko kuma ina tā da hankalin jama’a a majami’u ko kuwa wani wuri dabam a cikin birni ba.
13
Ba kuwa za su iya tabbatar maka ƙarar da suke yi yanzu a kaina ba.
14
Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa,
15
ina kuma da irin bege ɗaya ga Allah yadda mutanen nan suke da shi, cewa akwai tashin matattu masu adalci da masu mugunta duka.
16
Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane.
17
“Bayan ’yan shekaru da dama da ba na nan, sai na dawo Urushalima don in kawo wa mutanena kyautai saboda matalauta in kuma yi sadaka.
18
Ni tsarkake ne sa’ad da suka same ni cikin filin haikalin ina yin haka. Babu taro tare da ni, ba kuwa ina tā da hankali ba.
19
Amma akwai waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya, waɗanda ya kamata suna a nan a gabanka su kawo ƙara in suna da wani a kaina.
20
Ko kuwa waɗannan da suke a nan su faɗi laifin da suka same ni da shi sa’ad da na tsaya a gaban Majalisa,
21
sai ko wannan abu ɗaya kaɗai da na ɗaga murya na faɗi yayinda nake tsaye a gabansu cewa, ‘A game da tashin matattu ake mini shari’a a gabanku yau.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options