Ayyukan Manzanni 2:1-11
1
Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya.
2
Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.
3
Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.
4
Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.
5
To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.
6
Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa.
7
Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne?
8
To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa?
9
Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,
10
Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma
11
(Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”
Settings