Skip to content
Ayyukan Manzanni 19:8-20

Ayyukan Manzanni 19:8-20

8
Bulus ya shiga majami’a ya yi magana gabagadi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah.
9
Amma waɗansunsu suka taurara; suka ƙi su gaskata kuma a gaban jama’a suka yi baƙar magana game da Hanyar. Bulus kuwa ya bar su. Ya tafi tare da almajirai ya dinga tattaunawa da su kullum a babban ɗakin jawabi na Tirannus.
10
Wannan ya ci gaba har shekara biyu, sai da ya sa dukan Yahudawa da Hellenawa da suke zaune a lardin Asiya suka ji maganar Ubangiji.
11
Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus,
12
har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.
13
Waɗansu Yahudawa masu yawo gari-gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa’azi, na umarce ku, ku fito.”
14
’Ya’ya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka.
15
Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?”
16
Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba.
17
Da Yahudawa da Hellenawan da suke zama a Afisa suka ji wannan labari sai duk tsoro ya kama su, aka kuwa darjanta sunan Ubangiji Yesu ƙwarai.
18
Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu.
19
Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jama’a. Sa’ad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimillar ta kai darik dubu hamsin.
20
Ta haka maganar Ubangiji ta bazu ko’ina ta kuma yi ƙarfi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options