Skip to content
Ayyukan Manzanni 15:7-21

Ayyukan Manzanni 15:7-21

7
Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.
8
Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.
9
Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya.
10
To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba?
11
A’a! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”
12
Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurinsu.
13
Da suka gama, sai Yaƙub ya yi magana ya ce, “’Yan’uwa, ku saurare ni.
14
Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Al’ummai su zama nasa.
15
Kalmomin annabawa sun yi daidai da wannan, kamar yadda yake a rubuce cewa,
16
“ ‘Bayan wannan zan koma in kuma sāke gina tentin Dawuda da ya rushe. Kufansa zan sāke gina, in kuma mai da shi,
17
don ragowar mutane su nemi Ubangiji, kuma duk Al’umman da suke kira bisa sunana, in ji Ubangiji, wanda yake yin waɗannan abubuwa’
18
da aka sani tun zamanai.
19
“Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah.
20
A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini.
21
Gama Musa ya yi wa’azi a kowace birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majami’u kowane Asabbaci.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options