Tsallake zuwa abun ciki
Ayyukan Manzanni 10:19-33

Ayyukan Manzanni 10:19-33

19
Yayinda Bitrus yana cikin tunani game da wahayin, sai Ruhu ya ce masa, “Siman, ga mutum uku suna nemanka.
20
Saboda haka ka tashi ka sauka. Kada ka yi wata-wata, gama ni ne na aiko su.”
21
Sai Bitrus ya sauka ya ce wa mutanen, “Ni ne kuke nema. Me ya kawo ku?”
22
Mutanen suka amsa, “Mun zo ne daga wurin Korneliyus wani jarumin. Shi mutum ne mai adalci mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa ke girmamawa. Wani mala’ika mai tsarki ya faɗa masa, yă sa ka zo gidansa don yă ji abin da za ka faɗa.”
23
Sai Bitrus ya gayyaci mutanen cikin gida su zama baƙinsa. Kashegari Bitrus ya tafi tare da su, waɗansu ’yan’uwa daga Yoffa kuwa suka tafi tare da shi.
24
Kashegari sai ya iso Kaisariya. Korneliyus kuwa yana nan yana jiransu, ya kuma gayyaci ’yan’uwansa da abokansa na kusa.
25
Da Bitrus ya shiga gidan, Korneliyus ya sadu da shi ya kuma fāɗi a gabansa cikin bangirma.
26
Amma Bitrus ya sa shi ya tashi. Ya ce, “Tashi, ni mutum ne kawai.”
27
Yana magana da shi, sai Bitrus ya shiga ciki ya kuma tarar da taron mutane da yawa.
28
Sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san cewa dokarmu ta hana mutumin Yahuda yin cuɗanya, ko ya ziyarci Ba’al’umme. Amma Allah ya nuna mini cewa kada in kira wani mutum marar tsarki ko marar tsabta.
29
Don haka sa’ad da aka aika in zo, na zo ba wata faɗa. To, ko zan san abin da ya sa ka aika in zo?”
30
Korneliyus ya amsa ya ce, “Kwana huɗu da suka wuce ina a gidana ina addu’a a wannan lokaci, wajen ƙarfe uku na yamma. Ba zato ba tsammani sai ga wani mutum cikin tufafi masu walƙiya ya tsaya a gabana
31
ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji addu’arka, ya kuma tuna da kyautanka ga matalauta.
32
Ka aika zuwa Yoffa don a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. Shi baƙo ne a gidan Siman mai aikin fatu, wanda yake zama a bakin teku.’
33
Saboda haka na aika a zo da kai nan da nan, ya kuma yi kyau da ka zo. To ga mu duka a nan a gaban Allah don mu saurari dukan abin da Ubangiji ya umarce ka ka faɗa mana.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options