2 Sama’ila 6:1-7
1
Dawuda ya sāke tattara zaɓaɓɓun mutanen Isra’ila, dubu talatin.
2
Shi, da dukan mutanensa suka tashi daga Ba’ala-Yahuda don su hauro da akwatin alkawarin Allah, wanda ake kira da SunanUbangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a tsakanin kerubobin da suke a kan akwatin alkawarin.
3
Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah a sabuwar keken yaƙi, suka kawo shi daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Uzza da Ahiyo, ’ya’yan Abinadab maza, suka bi da keken yaƙin da akwatin alkawarin Allah yake ciki suka bi da keken yaƙin
4
da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo kuwa yana tafiya a gaban Abinadab.
5
Dawuda da dukan gidan Isra’ila suka yi biki sosai da dukan ƙarfinsu a gaban Ubangiji, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da ganguna, da kacau-kacau da kuma kuge.
6
Da suka kai masussukar Nakon, sai Uzza ya miƙa hannu don yă riƙe akwatin alkawarin Allah, gama shanun sun yi tuntuɓe.
7
Fushin Ubangiji kuwa ya ƙuna a kan Uzza domin aikin rashin bangirma, saboda haka Allah ya buge shi ya kuma mutu a can kusa da akwatin alkawarin Allah.
Settings