2 Sama’ila 5:17-25
17
Da Filistiyawa suka ji labari an shafe Dawuda sarki a bisa Isra’ila, sai suka haura da ƙarfi sosai don su nema shi, amma Dawuda ya ji labarin sai ya gangara zuwa mafaka.
18
To, fa, Filistiyawa suka zo suka baje ko’ina a cikin Kwarin Refayim;
19
saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In tafi in kai wa Filistiya hari? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Je ka, gama tabbatacce zan bashe Filistiyawa a hannunka.”
20
Saboda haka Dawuda ya tafi Ba’al-Ferazim, a can ya ci su da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa yakan fasu, haka Ubangiji ya kakkarya abokan gābana a gabana.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim.
21
Filistiyawa suka bar gumakansu a can, Dawuda da mutanensa kuwa suka kwashe su.
22
Har yanzu Filistiyawa suka sāke haurawa suka bazu a Kwarin Refayim;
23
saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji, ya kuwa ce, “Kada ka haura kai tsaye, amma ka kewaya ta bayansu ka fāɗa musu a gaban itatuwan balsam.
24
Da zarar ka ji tafiya kamar na takawar sojoji tana a bisan itatuwan balsam, sai ka yi maza, gama wannan alama ce cewa Ubangiji ya sha gabanka don yă karkashe sojojin Filistiyawa.”
25
Saboda haka Dawuda ya aikata yadda Ubangiji ya umarce shi, ya kuma karkashe Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.
Settings