2 Sama’ila 17:17-20
17
Yonatan da Ahimawaz suna zaune a En Rogel. Wata baranya ce za tă je ta faɗa musu, su kuma su tafi su gaya wa Sarki Dawuda don suna tsoro kada a ga suna shiga birnin.
18
Amma wani saurayi ya gan su, ya gaya wa Absalom. Sai dukansu biyu suka tashi da sauri suka shiga gidan wani mutum a Bahurim. Yana da rijiya a cikin gida, sai suka shiga cikinta.
19
Matarsa mutumin kuwa ta kawo tabarma ta shimfiɗa a bakin rijiyar, sai ta kawo hatsi ta baza a kanta. Ba kuwa wanda ya san abin da ta yi.
20
Da mutanen Absalom suka zo wurin matan a gidan, suka ce, “Ina Yonatan da Ahimawaz?” Matar ta ce, “Tuni, sun haye rafi.” Sai mutanen suka yi ta nemansu amma ba su ga kowa, sai suka koma Urushalima.
Settings