Skip to content
2 Sama’ila 15:13-23

2 Sama’ila 15:13-23

13
Wani manzo ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Zukatan mutanen Isra’ila sun koma wajen Absalom.”
14
Sai Dawuda ya ce wa dukan fadawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Ku zo! Mu gudu, in ba haka ba, babu wanda zai tsira daga hannun Absalom. Dole mu bar nan, nan da nan, in ba haka ba zai tashi da sauri yă fāɗa mana, yă kuma hallaka garin da takobi.”
15
Sai fadawan sarki suka ce masa, “Barorinka suna a shirye su yi duk abin da ranka yă daɗe, ya zaɓa.”
16
Sarki ya kama hanya, dukan gidansa kuwa suna biye da shi; amma ya bar ƙwarƙwarai goma su lura da fada.
17
Ta haka sarki ya kama hanya da dukan mutane suna biye da shi, suka yi sansani a wani wuri mai ɗan nisa da Urushalima.
18
Dukan mutanensa suka wuce gabansa, tare da dukan Keretawa da Feletiyawa; da dukan mutane ɗari shida na Gittiyawan da suka raka shi daga Gat, suka wuce gaban sarki.
19
Sarki ya ce wa Ittai mutumin Gat, “Don me za ka zo tare da mu? Ka koma ka zauna tare da Sarki Absalom. Kai baƙo ne, ɗan gudun hijira daga garinka.
20
Jiya-jiya ka zo. Yau kuma in sa ka yi ta yawo tare da mu, ga shi ban ma san inda za ni ba? Koma, ka tafi da ’yan’uwanka. Bari alheri da amincin Ubangiji su kasance tare da kai.”
21
Amma Ittai ya ce wa sarki, “Muddin Ubangiji yana a raye kuma muddin ranka yă daɗe yana a raye, duk inda ranka yă daɗe sarki zai kasance, ko a yi rai ko a mutu, a can bawanka zai kasance.”
22
Dawuda ya ce wa Ittai, “Wuce gaba, taka mu je.” Sai Ittai mutumin Gat ya shiga layi tare da dukan mutanensa da iyalan da suke tare da shi.
23
Dukan ƙauyuka suka yi ta kururuwa yayinda mutanen suke wucewa. Sarki shi ma ya haye ta Kwarin Kidron, mutane kuma suka ci gaba da tafiya zuwa wajen hamada.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options