Tunatarwa da Gargaɗi Game da Masu Ba’a
1
Abokaina ƙaunatattu, wannan ita ce wasiƙata ta biyu gare ku. Na rubuta su biyun su zama abin tuni don su faɗakar da ku ga tunani mai kyau.
2
Ina so ku tuna da kalmomin da annabawa masu tsarki na dā suka faɗa da kuma umarnin da Ubangijinmu da Mai Cetonmu ya bayar ta wurin manzanninku.
3
Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu.
4
Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.”
5
Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma.
6
Ta wurin waɗannan ruwan ne aka nutsar, aka kuma hallakar da duniya ta wancan lokaci.
7
Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.