Skip to content
2 Sarakuna 9:13-22

2 Sarakuna 9:13-22

13
Sai suka yi sauri suka ɗauki rigunansu suka shimfiɗa a ƙasa, suka busa kakaki, suka yi ihu, suka ce, “Yehu ne sarki.”
14
Saboda haka, Yehu ɗan Yehoshafat, ɗan Nimshi, ya ƙulla wa Yoram maƙarƙashiya (To, Yoram da dukan Isra’ila suna kāre Ramot Gileyad daga Hazayel sarkin Aram,
15
amma Sarki Yoram ya koma Yezireyel don yă farfaɗo daga raunukan da Arameyawa suka ji masa a wata gabzawar da ya yi da Hazayel sarkin Aram.) Yehu ya ce, “In haka kuke ji, kada ku bar wani yă sulluɓe daga birnin yă kai labarin Yezireyel.”
16
Sai ya tashi ya ɗauki keken yaƙinsa ya tafi Yezireyel gama Yoram yana hutawa a can. Ga kuma Ahaziya sarkin Yahuda ya je don yă gan shi.
17
Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezireyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa’ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.” Sai Yoram ya umarta, “Nemi mahayin doki a aike shi yă tarye su, yă kuma tambaye su, ‘Lafiya?’ ”
18
Sai mahayin dokin ya hau, ya ruga, ya taryi Yehu, ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Sai Yehu ya ce masa, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.” Sai mai tsaron ya ce wa sarki, “Ɗan saƙon ya kai wurinsu, amma ba ya dawowa.”
19
Saboda haka sarki ya sāke aika mahayin doki na biyu. Sa’ad da ya isa wurinsu sai ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Yehu ya ce, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.”
20
Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma shi ma ba ya dawowa. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa kamar mahaukaci.”
21
Yoram ya umarta, “Haɗa mini keken yaƙi!” Da aka haɗa, sai Yoram sarkin Isra’ila, da Ahaziya sarkin Yahuda, suka hau suka tafi, kowa a keken yaƙinsa, don su taryi Yehu. Suka sadu da shi a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel.
22
Sa’ad da Yoram ya ga Yehu sai ya tambaye shi, “Lafiya kuwa ka zo, Yehu?” Yehu ya ce, “Ina kuwa lafiya, da yake dukan bautar gumaka da bokancin mahaifiyarka Yezebel sun bazu ko’ina?”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options