2 Sarakuna 9:1-10
1
Sai Elisha ya kira wani daga cikin ƙungiyar annabawa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kwalabar mai ka je Ramot Gileyad.
2
Da ka isa can, ka nemi Yehu ɗan Yehoshafat, ɗan Nimshi. Ka je wurinsa, ka ja shi gefe daga abokansa, ka shiga da shi ɗaki na ciki.
3
Sa’an nan ka ɗauki kwalabar man ka zuba a kansa, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, na naɗa ka sarkin Isra’ila.’ Sa’an nan ka buɗe ƙofa ka ruga a guje; kada ka ɓata lokaci!”
4
Sai saurayin nan, annabi, ya tafi Ramot Gileyad.
5
Da ya isa can, sai ya tarar da hafsoshin soji zaune a wuri guda. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka komanda.” Sai Yehu ya ce, “Wanne a cikinmu?” Sai ce, “Dominka, komanda.”
6
Sai Yehu ya tashi ya shiga cikin gida. Sa’an nan annabin ya zuba wa Yehu mai a kā, ya ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na naɗa ka sarki a bisa jama’ar Ubangiji, wato, Isra’ila.
7
Za aka hallaka gidan Ahab maigidanka, zan kuma ɗauki fansar jinin bayina annabawa da kuma jinin dukan bayin Ubangiji da Yezebel ta zub da.
8
Dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan kashe dukan ’ya’yan Ahab maza a Isra’ila, bayi ko ’yantattu.
9
Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat da kuma kamar gidan Ba’asha ɗan Ahiya.
10
Game da Yezebel kuwa, karnuka za su cinye ta a fili a Yezireyel, ba kuwa wanda zai binne ta.’ ” Sa’an nan ya buɗe ƙofa ya ruga a guje.
Settings