Skip to content
2 Sarakuna 2:9-15

2 Sarakuna 2:9-15

9
Da suka haye, sai Iliya ya ce wa Elisha, “Faɗi mini, abin da kake so in yi maka kafin a ɗauke ni daga gare ka!” Elisha ya amsa ya ce, “Bari in gāji ninki biyu na ruhunka.”
10
Iliya ya ce, “Ka nemi abu mai wuya, amma in ka ga lokacin da aka ɗauke ni daga gare ka, zai zama naka, in ba haka ba, ba za ka samu ba ke nan.”
11
Yayinda suke tafiya suna magana, sai kwatsam, keken yaƙin wuta da dawakan wuta suka ratse tsakaninsu, sai Iliya ya tafi sama a cikin guguwa.
12
Da Elisha ya ga haka sai ya yi ihu yana cewa, “Babana! Babana! Kekunan yaƙin da mahayan dawakan Isra’ila!” Elisha kuwa bai sāke ganinsa ba. Sai ya kama tufafinsa ya yayyage.
13
Sai ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya koma ya tsaya a gaɓar Kogin Urdun.
14
Sa’an nan Elisha ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya bugi ruwan da shi. Ya ce, “Yanzu ina Ubangiji Allah na Iliya?” Da ya bugi ruwan sai ruwan ya dāre gida biyu, sai ya haye.
15
Ƙungiyar annabawa daga Yeriko, waɗanda suke kallo, suka ce, “Ruhun Iliya yana a kan Elisha.” Sai suka je su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options