2 Sarakuna 17:6-18
6
A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, sarkin Assuriya ya ci Samariya da yaƙi ya kuma kwashe Isra’ilawa zuwa Assuriya. Ya tsugunar da su a Hala, da a Gozan a bakin Kogin Habor da kuma a garuruwan Medes.
7
Duk wannan ya faru ne saboda Isra’ilawa sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fitar da su daga Masar daga ƙarƙashin ikon Fir’auna sarkin Masar. Sun yi wa waɗansu alloli sujada
8
suka kuma bi gurbin al’umman da Ubangiji ya kora a gabansu, da kuma ayyukan da sarakuna Isra’ila suka gabatar.
9
Isra’ilawa a ɓoye sun aikata abubuwan da ba daidai ba ga Ubangiji Allahnsu. Tun daga hasumiyoyi har zuwa birane masu katanga, sun gina wa kansu wuraren sujada na tudu a dukan garuruwansu.
10
Suka kafa keɓaɓɓun duwatsu da kuma ginshiƙan Ashera a kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane babban itace.
11
Suka ƙona turare a kan kowane tudu, kamar dai yadda al’umman da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka yi muguntan da ya sa Ubangiji ya yi fushi.
12
Suka bauta wa gumaka, ko da yake Ubangiji ya ce, “Ba za ku yi wannan ba.”
13
Ubangiji ya yi wa Isra’ila da Yahuda kashedi ta bakin dukan annabawansa da kuma masu duba, cewa, “Ku juyo daga mugayen ayyukanku. Ku yi biyayya da umarnai da farillaina, bisa ga dukan Dokar da na dokaci kakanninku su bi, waɗanda na kuma bayar ta wurin bayina, annabawa.”
14
Amma ba su saurare ni ba don sun kangare kamar kakanninsu, waɗanda ba su amince da Ubangiji Allahnsu ba.
15
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.
16
Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada.
17
Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi.
18
Saboda haka Ubangiji ya yi fushi ƙwarai da Isra’ila, ya kuma kawar da su daga gabansa. Kabilar Yahuda kaɗai aka bari,
Settings