2 Sarakuna 17:32-38
32
Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma suka zaɓi mutanensu su yi musu hidima a matsayin firistoci a masujadan da suke kan tuddai.
33
Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma sun bauta wa allolinsu bisa ga al’adun ƙasashen da suka fito.
34
Har yă zuwa yau, sun nace da ayyukansu na dā. Ba sa yin wa Ubangiji sujada, ba sa kuma bin dokoki da farillansa, dokoki da umarnan da Ubangiji ya ba wa zuriyar Yaƙub, wadda ya ba wa suna Isra’ila.
35
Da Ubangiji ya ƙulla alkawari da Isra’ilawa, ya dokace su cewa, “Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada ko ku durƙusa a gabansu ku bauta musu, ko ku miƙa musu hadaya.
36
Amma Ubangiji wanda ya fito da ku daga Masar da iko mai girma da hannu mai ƙarfi, shi ne za ku yi masa sujada. Gare shi za ku durƙusa ku kuma miƙa masa hadayu.
37
Dole kullum ku mai da hankali ga kiyaye ƙa’idodi da farillan, dokoki da umarnan da ya rubuta muku. Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada.
38
Kada ku manta da alkawarin da na ƙulla da ku, kada ku yi sujada ga waɗansu alloli.
Settings