Skip to content
2 Sarakuna 14:23-28

2 Sarakuna 14:23-28

23
A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yehowash sarkin Isra’ila ya zama sarki a Samariya, ya kuma yi mulki na shekaru arba’in da ɗaya.
24
Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji bai kuwa kauce wa duk zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba.
25
Shi ne ya maido da iyakokin Isra’ila daga Lebo Hamat zuwa Tekun Araba, bisa ga maganar Ubangiji, Allah na Isra’ila, da ya yi ta bakin bawansa Yunana ɗan Amittai, annabi daga Gat-Hefer.
26
Ubangiji ya ga irin muguwar wahalar da ta shafi kowa a Isra’ila, ko bawa ko ’yantacce, babu mai taimakonsu.
27
Da yake kuma Ubangiji bai ce zai shafe sunan Isra’ila daga fuskar duniya ba, sai ya cece su ta hannun Yerobowam ɗan Yowash.
28
Game da sauran ayyukan mulkin Yerobowam, da dukan abin da ya yi, da yaƙe-yaƙen da ya yi, haɗe da sāke ƙwato wa Isra’ila Damaskus da Hamat waɗanda suke a hannun Yahuda, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options