2 Korintiyawa 9:1-5
1
Babu wata bukata in rubuta muku game da hidiman nan ga tsarkaka.
2
Gama na san aniyarku na yin taimako, ina kuma taƙama a kan wannan ga Makidoniyawa, ina faɗin musu cewa tun bara, ku da kuke a Akayya a shirye kuke ku bayar. Ƙoƙarinku kuwa ya zuga yawancinsu ga aiki.
3
Amma ina aika ’yan’uwan nan don kada taƙamar da muke yi da ku, a kan wannan al’amari ta zama a banza, sai dai domin yă zama kuna nan a shirye, kamar yadda na faɗa za ku kasance.
4
Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku.
5
Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba.
Settings