Skip to content
2 Korintiyawa 12:1-10

2 Korintiyawa 12:1-10

1
Dole in ci gaba da yin taƙama. Ko da yake ba za tă amfane ni ba, zan yi magana a kan ru’uyoyi da wahayoyi waɗanda na karɓa daga Ubangiji.
2
Na san wani a cikin Kiristi wanda shekaru goma sha huɗu da suka wuce an ɗauke zuwa sama ta uku. Ko a cikin jiki ne, ko kuwa ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, Allah ne ya sani.
3
Na kuma san cewa wannan mutum, ko a cikin jiki ne, ko kuma ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, amma Allah ne ya sani,
4
an ɗauke shi ne zuwa aljanna. Ya ji waɗansu abubuwa waɗanda ba zai iya faɗarsu da kalmomi ba, abubuwan da ba a ba wa mutum damar faɗi.
5
Zan yi taƙama game da mutum irin wannan, sai dai ni ba zan yi taƙama da kaina ba, sai dai a kan rashin ƙarfina.
6
Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata.
7
Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni.
8
Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu.
9
Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.
10
Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options