2 Tarihi 32:14-17
14
Wanne a cikin dukan allolin waɗannan ƙasashe da kakannina suka hallaka ya taɓa iya ceton mutanensa daga gare ni? To, yaya Allahnku zai iya cetonku daga hannuna?
15
Yanzu fa, kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku yă kuma ɓad da ku haka. Kada ku gaskata shi, gama babu allahn wata ƙasa ko masarautar da ya taɓa iya ceton mutanensa daga hannuna ko kuwa hannun kakannina. Balle har Allahnku yă cece ku daga hannuna!”
16
Hafsoshin Sennakerib suka ci gaba da maganar banza wa Ubangiji Allah da kuma a kan bawansa Hezekiya.
17
Sarki ya kuma rubuta wasiƙu yana zagin Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana faɗin wannan a kansa, “Kamar yadda sauran allolin mutanen sauran ƙasashe ba su iya kuɓutar da mutane daga hannuna ba, haka Allahn Hezekiya ba zai kuɓutar da mutanensa daga hannuna ba.”
Settings