Skip to content
2 Tarihi 31:2-11

2 Tarihi 31:2-11

2
Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi-kashi, kowanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima, su yi godiya, su kuma rera yabai a ƙofofin mazaunin Ubangiji.
3
Sarki ya ba da taimako daga mallakarsa domin hadayun ƙonawa, safe da yamma da kuma don hadayun ƙonawa a Asabbatai, Sabon Wata da kuma ƙayyadaddun bukukkuwa kamar yadda yake a rubuce a cikin Dokar Ubangiji.
4
Ya umarci mutanen da suke zama a Urushalima su ba da rabon da yake na firistoci da Lawiyawa, don su ƙwallafa ransu ga Dokar Ubangiji.
5
Nan da nan aka baza umarnin, sai Isra’ilawa suka bayar ’ya’yan farin hatsinsu, sabon ruwan inabi, mai da kuma zuma da dukan abin da gona ta bayar, hannu sake. Suka kawo zakan kowane abu da yawa.
6
Mutanen Isra’ila da Yahuda waɗanda suke zama a garuruwan Yahuda, su ma suka kawo zakan shanu da na tumaki da kuma zakan abubuwa masu tsarki da aka keɓe ga Ubangiji Allahnsu, suka jibge su tsibi-tsibi.
7
Sun fara yin haka a wata na uku, suka kuma gama a wata na bakwai.
8
Sa’ad da Hezekiya da fadawansa suka zo suka ga tsibin, sai suka yabi Ubangiji, suka kuma albarkace mutanensa Isra’ila.
9
Hezekiya ya tambayi firistoci da Lawiyawa game da tsibin;
10
sai Azariya babban firist, daga iyalin Zadok ya amsa, “Tun daga lokacin da mutane suka fara kawo taimakonsu ga haikalin Ubangiji, muna da isashe don abinci da kuma da yawa da za mu rage, domin Ubangiji ya albarkaci mutanensa, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.”
11
Hezekiya ya ba da umarni a shirya ɗakunan ajiya a haikalin Ubangiji, aka kuwa yi haka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options