Skip to content
2 Tarihi 31:14-19

2 Tarihi 31:14-19

14
Kore ɗan Imna Balawe, mai tsaron Ƙofar Gabas, shi ne yake lura da baikon yardan ran da aka yi wa Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki.
15
Eden, Miniyamin, Yeshuwa, Shemahiya, Amariya da Shekaniya sun taimake shi da aminci a cikin garuruwan firistoci, suna ba da rabo wa ’yan’uwansu firistoci bisa ga sassansu, tsofaffi da yara.
16
Bugu da ƙari, suka ba da rabo ga maza ’yan shekaru uku ko fiye waɗanda sunayensu suna a tarihin zuriya, dukan waɗanda ba za su iya shiga haikalin Ubangiji su yi ayyukansu na kullum ba, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu.
17
Suka kuma ba da rabo ga firistocin da aka rubuta ta iyalansu cikin tarihin zuriya, haka kuma ga Lawiyawa masu shekara ashirin ko fiye, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu.
18
Suka haɗa da dukan ƙanana ’ya’yansu, mata, da kuma ’ya’ya maza da ’ya’ya mata, al’umma gaba ɗaya da aka jera a waɗannan tarihin zuriya. Gama sun yi aminci cikin tsarkake kansu.
19
Akwai mutane a garuruwa da yawa waɗanda aka sa don su rarraba wa ’ya’yan Haruna, firist, maza, waɗanda suke zaune a gonaki na ƙasar garuruwansu su ba kowane namijin da aka rubuta na Lawiyawa, rabonsa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options