Skip to content
2 Tarihi 24:23-27

2 Tarihi 24:23-27

23
Da shekara ta kewaye, mayaƙan Aram suka yi gāba da Yowash suka kai hari wa Yahuda da Urushalima suka kuma kashe dukan shugabannin mutane, suka aika da dukan ganima zuwa ga sarkinsu a Damaskus.
24
Ko da yake mayaƙan Arameyawa sun zo da mutane kaɗan kawai, Ubangiji ya sa suka ci nasara a kan sojojin Yahuda mafi yawa, don mutanen Yahuda sun rabu da Ubangiji Allah na kakanninsu, aka kuma hukunta Yowash.
25
Sa’ad da Arameyawa suka janye, suka bar Yowash da mummunan rauni. Hafsoshinsa suka haɗa baki a kansa saboda kisan ɗan Yehohiyada firist da ya yi, suka kashe shi a kan gadonsa. Ta haka ya mutu aka kuma binne shi makabartan sarakuna.
26
Waɗanda suka haɗa bakin kuwa su ne Zabad ɗan Shimeyat wata mutuniyar Ammon da Yehozabad ɗan Shimrit wata mutuniyar Mowab.
27
Labarin ’ya’yansa maza, annabce-annabce masu yawa game da shi, da tarihin gyaran haikalin Allah suna a rubuce a rubuce-rubuce a littafin sarakuna. Amaziya ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options