Skip to content
2 Tarihi 24:15-22

2 Tarihi 24:15-22

15
Yanzu Yehohiyada ya tsufa kuma cike da shekaru, ya kuwa mutu yana da shekara ɗari da talatin.
16
Aka binne shi tare da sarakuna a cikin Birnin Dawuda, saboda kirkin da ya yi a Isra’ila wa Allah da haikalinsa.
17
Bayan mutuwar Yehohiyada, hafsoshin Yahuda suka zo suka yi mubaya’a wa sarki, ya kuma saurare su.
18
Suka yashe haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa ginshiƙan Ashera da kuma gumaka. Saboda laifinsu, fushin Allah ya sauko a kan Yahuda da Urushalima.
19
Ko da yake Ubangiji ya aiki annabawa zuwa wurin mutane don su dawo da su gare shi, kuma ko da yake sun ba da shaida a kansu, ba su saurara ba.
20
Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Zakariya ɗan Yehohiyada firist. Ya tsaya a gaban mutane ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Me ya sa ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji ba? Ba za ku yi nasara ba. Domin kun yashe Ubangiji, shi ma ya yashe ku.’ ”
21
Amma suka yi masa maƙarƙashiya, kuma ta wurin umarnin sarki suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu a filin haikalin Ubangiji.
22
Sarki Yowash bai tuna da alherin da Yehohiyada mahaifin Zakariya ya nuna masa ba, sai ya kashe ɗansa, wanda ya ce yayinda yake mutuwa, “Bari Ubangiji yă dubi wannan yă kuma sāka maka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options