2 Tarihi 23:14-21
14
Yehohiyada firist ya fito da shugabanni waɗanda suke shugabancin rundunar sojoji, ya ce musu, “Ku fitar da ita tsakanin sojoji ku kuma kashe duk wanda ya bi ta da takobi.” Gama firist ya ce, “Kada ku kashe ta a haikalin Ubangiji.”
15
Saboda haka suka kama ta yayinda take kaiwa mashigin Ƙofar Doki a filin fada, a can suka kashe ta.
16
Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari cewa shi da mutane da kuma sarki za su zama mutanen Ubangiji.
17
Dukan mutane suka tafi haikalin Ba’al suka rurrushe shi. Suka farfashe bagadan da gumakan, suka kuma kashe Mattan firist na Ba’al a gaban bagadan.
18
Sa’an nan Yehohiyada ya sa aikin lura da haikalin Ubangiji a hannuwan firistoci, waɗanda suke Lawiyawan da Dawuda ya ba su aikin haikali don su miƙa hadayun ƙonawa na Ubangiji kamar yadda yake a rubuce a Dokar Musa, da farin ciki da kuma rerawa, kamar yadda Dawuda ya umarta.
19
Ya kuma sa matsaran ƙofofi a ƙofofin haikalin Ubangiji don kada wani da ba shi da tsarki yă shiga.
20
Ya ɗauki shugabannin ɗari-ɗari, manyan gari, shugabannin mutane da dukan mutanen ƙasar tare da shi ya saukar da sarki daga haikalin Ubangiji. Suka shiga fada ta Ƙofar Bisa suka kuma zaunar da sarki a kujerar sarauta,
21
sai dukan mutanen ƙasar suka yi farin ciki. Birnin kuwa ya samu zaman lafiya domin an kashe Ataliya da takobi.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings