2 Tarihi 21:1-3
1
Yehoshafat ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
2
’Yan’uwan Yehoram, ’ya’yan Yehoshafat maza su ne, Azariya, Yehiyel, Zakariya, Azariyahu, Mika’ilu da Shefatiya. Dukan waɗannan su ne ’ya’yan Yehoshafat sarkin Isra’ila maza.
3
Mahaifinsu ya ba su kyautai masu yawa na azurfa da zinariya da kayayyaki masu daraja, tare da birane masu katanga a Yahuda, amma ya ba da mulki ga Yehoram domin shi ne ɗan farinsa.
Settings