2 Tarihi 18:12
Ana nuna aya 12 tare da mahallin da ke kewaye.
9
Saye da rigunan sarakuna, sarki Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zaune a kan kujerunsu na mulki a masussuka ta ƙofar shigar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu.
10
To, fa, Zedekiya ɗan Kena’ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka sassoki Arameyawa sai sun hallaka.’ ”
11
Dukan sauran annabawan suka yi irin annabcin nan. Suka ce, “A haura zuwa Ramot Gileyad a yi nasara, gama Ubangiji zai ba da shi cikin hannun sarki.”
12
Ɗan saƙon da ya tafi don yă kawo Mikahiya kuwa ya ce masa, “Duba, kowannen a cikin annabawa ya yi faɗin nasara wa sarki. Don haka kai ma ka yi maganar da za tă gamshi sarki kamar yadda suka yi.”
13
Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji, zan faɗa masa kawai abin da Allahna ya faɗa.”
14
Da suka iso, sarki ya tambaye shi, “Mika, mu tafi mu yaƙi Ramot Gileyad, ko kada mu tafi?” Ya amsa, “Kai masa yaƙi za ka kuwa yi nasara, gama za a ba da su a hannunka.”
15
Sarki ya ce masa, “Sau nawa zan sa ka rantse don ka faɗa gaskiya a cikin sunan Ubangiji?”
Settings