2 Tarihi 12:13-16
13
Sarki Rehobowam ya kafa kansa daram a Urushalima, ya kuma ci gaba a matsayin sarki. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila wanda zai sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama ce, ita mutuniyar Ammon ce.
14
Ya aikata mugunta domin bai sa zuciyarsa ga neman Ubangiji ba.
15
Game da ayyukan mulkin Rehobowam, daga farko zuwa ƙarshe, ba a rubuce suke a tarihin Shemahiya annabi da Iddo mai gani wanda yake zancen zuriyoyi ba? Aka kasance da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam.
16
Rehobowam ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Abiya ɗansa kuma ya gāje shi a matsayin sarki.
Settings