2 Tarihi 11:14
Ana nuna aya 14 tare da mahallin da ke kewaye.
11
Ya ƙarfafa kāriyarsu ya kuma sa shugabannin mayaƙa a cikinsu, tare da tanadin abinci, man zaitun da kuma ruwan inabi.
12
Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.
13
Firistoci da Lawiyawa daga dukan yankuna ko’ina a Isra’ila suka haɗa kai da shi.
14
Lawiyawa suka ma bar makiyayansu da mallakarsu, suka zo Yahuda da Urushalima domin Yerobowam da ’ya’yansa maza sun ƙi su a matsayin firistocin Ubangiji.
15
Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi.
16
Waɗanda suke daga kowane kabilar Isra’ila waɗanda suka sa zuciya a kan neman Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima don su miƙa hadayu ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
17
Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci.
Settings