Skip to content
1 Timoti 3:8-13

1 Timoti 3:8-13

8
Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba.
9
Dole su riƙe asirin bangaskiya su kuma kasance da lamiri mai tsabta.
10
Dole a fara gwada su tukuna; sa’an nan in ba a sami wani abin zargi game da su ba, sai su shiga aikin masu hidima.
11
A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome.
12
Dole mai hidimar ikkilisiya yă zama mijin mace guda dole kuma yă iya tafiyar da ’ya’yansa da kuma iyalinsa da kyau.
13
Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options