1 Sama’ila 26:7-11
7
Saboda haka Dawuda da Abishai suka gangara zuwa wurin rundunar da dare, sai ga Shawulu kwance yana barci a cikin sansani da māshinsa a kafe a ƙasa kusa da kansa. Abner kuwa tare da sojoji suna kwance kewaye da shi.
8
Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Allah ya ba da maƙiyinka a hannunka. Bari in kafe shi da ƙasa da māshina, zan soke shi da māshi sau ɗaya tak, ba na bukata in soke shi sau biyu.”
9
Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi. Wa zai sa hannu a kan shafaffe na Ubangiji, har yă tsira?
10
Muddin Ubangiji yana a raye, Ubangiji da kansa zai buge shi, ko yă mutu a lokacinsa, ko kuma yă mutu a wurin yaƙi.
11
Amma Allah yă sawwaƙa in sa hannu a shafaffen Ubangiji, ka ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da kansa mu tafi.”
Settings