1 Sama’ila 19:17-21
17
Shawulu ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya gudu ya tsere?” Mikal ta ce masa, “Ya ce mini, ‘Idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni?’ ”
18
Da Dawuda ya gudu ya tsere, sai ya tafi wurin Sama’ila a Rama ya gaya masa dukan abin da Shawulu ya yi masa. Da shi da Sama’ila suka tafi Nayiwot suka zauna a can.
19
Shawulu ya sami labari cewa, “Dawuda yana Nayiwot a Rama.”
20
Sai ya aiki mutane su je su kamo Dawuda, amma da suka ga ƙungiyar annabawa suna annabci tare da Sama’ila shugabansu a tsaye, sai Ruhun Allah ya sauko wa mutanen Shawulu, su ma suka fara yin annabci.
21
Shawulu ya sami labari game da wannan, sai ya sāke aiken waɗansu da yawa. Su ma suka shiga yin annabci. Shawulu ya sāke aiken mutane sau na uku, su kuma suka shiga yin annabci.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings