Skip to content
1 Sama’ila 19:1-7

1 Sama’ila 19:1-7

1
Shawulu ya gaya wa ɗansa Yonatan da ma’aikatansa su kashe Dawuda. Amma Yonatan yana son Dawuda sosai.
2
Sai ya gargaɗe shi ya ce, “Mahaifina Shawulu yana neman hanyar da zai kashe ka. Ka kula da kanka gobe da safe, ka tafi wani wuri ka ɓuya.
3
Zan je in tsaya da mahaifina a fili inda kake, zan yi masa magana game da kai. Zan kuma gaya maka abin da na ji.”
4
Yonatan ya yi magana mai kyau a kan Dawuda a wajen mahaifinsa ya ce, “Kada sarki yă yi wani mummunan abu wa bawansa Dawuda, gama bai yi maka wani abu marar kyau ba. Abin da ya yi ya amfane ka ƙwarai da gaske.
5
Ya yi kasai da ransa sa’ad da ya kashe Bafilistin nan. Ubangiji ya ba wa dukan Isra’ila babban nasara, ka gani, ka kuma yi farin ciki. Don me za ka ci mutuncin amintaccen mutum kamar Dawuda ta wurin kashe shi ba tare da wani dalili ba?”
6
Shawulu ya saurari Yonatan sai ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, ba za a kashe Dawuda ba.”
7
Ta haka Yonatan ya kira Dawuda ya gaya masa dukan maganarsu. Ya kawo shi wurin Shawulu, Dawuda kuwa ya zauna tare da Shawulu kamar dā.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options