1 Sama’ila 16:12-16
12
Sai ya aika aka kawo shi. Ga shi kuwa kyakkyawan saurayi ne mai kyan gani. Ubangiji ya ce, “Tashi ka shafe shi, shi ne wannan.”
13
Saboda haka Sama’ila ya ɗauko ƙahon nan da yake da mai ya shafe Dawuda a gaban ’yan’uwansa. Daga wannan rana kuwa ruhun Ubangiji ya sauko wa Dawuda da iko. Sai Sama’ila ya koma Rama.
14
To, fa, Ruhun Ubangiji ya riga ya rabu da Shawulu, sai mugun ruhu daga Ubangiji ya soma ba shi wahala.
15
Ma’aikatan Shawulu suka ce masa, “Duba, ga mugun ruhu daga Allah yana ba ka wahala.
16
Ranka yă daɗe, muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo wanda ya iya kiɗan molo, domin duk sa’ad da mugun ruhun nan daga Allah ya tashi, sai yă kaɗa molon don hankalinka yă kwanta.”
Settings