1 Sama’ila 1:17-24
17
Eli ya ce, “In haka ne, to, ki sauka lafiya, Allah na Isra’ila kuma yă ba ki abin da kika roƙa daga gare shi.”
18
Ta ce, bari baiwarka tă sami tagomashi a idonka. Sai ta yi tafiyarta ta je ta ci wani abu, fuskarta kuwa ba tă ƙara kasance da baƙin ciki ba.
19
Kashegari da sassafe suka tashi suka yi sujada a gaban Ubangiji, sai suka koma garinsu a Rama. Elkana kuwa ya kwana da matarsa Hannatu, Ubangiji kuma ya tuna da ita.
20
Ana nan sai Hannatu ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa. Ta ba shi suna Sama’ila; tana cewa, “Domin na roƙe shi daga wurin Ubangiji.”
21
Da shekara ta kewayo, sai Elkana da iyalinsa suka sāke tafi Shilo domin su yi hadaya ga Ubangiji, yă kuma cika alkawarin da ya yi.
22
Hannatu kuwa ba tă bi su ba. Ta gaya wa mijinta cewa, “Sai bayan na yaye yaron, zan kai shi in miƙa shi a gaban Ubangiji, yă kuma kasance a wurin koyaushe.”
23
Elkana mijinta ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi miki kyau. Ki jira har sai bayan kin yaye shi. Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Saboda haka matar ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta har ta yaye shi.
24
Bayan ta yaye shi, sai ta ɗauki yaron tare da bijimi bana uku, da mudun gari, da salkan ruwan inabi, ta kawo su a gidan Ubangiji a Shilo.
Settings