Skip to content
1 Bitrus 2:11-17

1 Bitrus 2:11-17

11
Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku.
12
Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.
13
Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane, ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko,
14
ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai.
15
Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci.
16
Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah.
17
Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa. Ku ƙaunaci ’yan’uwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options