Skip to content
1 Sarakuna 5:13-17

1 Sarakuna 5:13-17

13
Sarki Solomon ya ɗebi ma’aikata daga dukan Isra’ila, su dubu talatin.
14
Ya riƙa aika su dubu goma-goma zuwa Lebanon kowane wata, saboda su yi wata ɗaya a Lebanon, watanni biyu kuma a gida. Adoniram ne ya lura da aikin gandun.
15
Solomon ya kasance da ’yan ɗauko guda dubu saba’in da masu yankan duwatsu guda dubu tamanin a cikin tuddai,
16
ya kuma kasance da shugabanni dubu uku da ɗari uku waɗanda suke lura da aikin, su ne kuma suke bi da ma’aikatan.
17
Bisa ga umarnin sarki sai suka cire manyan duwatsu masu kyau don a tanada tushen duwatsun da aka gyara domin haikalin daga wurin haƙar duwatsun.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options