1 Sarakuna 4:1-19
1
Sai Sarki Solomon ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila.
2
Waɗannan su ne manyan shugabanninsa. Azariya ɗan Zadok shi ne firist;
3
Elihoref da Ahiya, ’ya’yan Shisha maza, su ne marubuta. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne mai lura da takardu.
4
Benahiya ɗan Yehohiyada, shi ne shugaban mayaƙa. Zadok da Abiyatar, su ne firistoci.
5
Azariya ɗan Natan, shi ne mai lura da shugabannin yanki. Zabud ɗan Natan, shi ne firist da kuma mai wa sarki shawara.
6
Ahishar, shi ne sarkin fada. Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura da aikin gandu.
7
Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.
8
Ga sunayensu, Ben-Hur, shi ne a ƙasar tudun Efraim;
9
Ben-Deker, shi ne a Makaz, Sha’albim, Bet-Shemesh da Elon Bet-Hanan;
10
Ben-Hesed, shi ne a Arubbot (Soko da dukan ƙasar Hefer);
11
Ben-Abinadab, shi ne a Nafot Dor (ya auri Tafat ’yar Solomon);
12
Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam;
13
Ben-Geber, shi ne a Ramot Gileyad (Mazaunan Yayir ɗan Manasse a Gileyad suna a ƙarƙashinsa, haka ma yankin Argob a Bashan tare da manyan biranen sittin masu katanga da suke da ƙyamare na tagulla);
14
Ahinadab ɗan Iddo, shi ne a Mahanayim;
15
Ahimawaz, shi ne a Naftali (ya auri Basemat ’yar Solomon);
16
Ba’ana ɗan Hushai, shi ne a Asher da Bayelot;
17
Yehoshafat ɗan Faruwa, shi ne a Issakar;
18
Shimeyi ɗan Ela, shi ne a Benyamin;
19
Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin.
Settings